19 Maris 2022 - 19:34
Ziyarar Bashar Assad A UAE Alama Ce Ta Samun Gagarumin Canji A Siyasar Kasa Da Kasa

A jiya Juma’a ne dai shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya kai ziyara kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, a ziyararsa ta farko a wata kasar Larabawa, tun bayan barkewar rikicin da kasashen ketare suka haifar a cikin kasar ta Syria, saboda wasu dalilai na siyasa.

A ganawarsa da Assad, Yarima mai jiran gado na Abu Dhabi, Sheikh Mohammed bin Zayed al-Nahya "ya jaddada cewa, Siriya wani ginshiki ne na tsaron kasashen Larabawa, inda ya ce kasarsa na burin ganin ta karfafa alakarta da kuma hadin gwiwa da kasarSiriya." Shi ma a nasa bangaren Bashar Assad ya bukaci da cewa, domin kare yankin gabas ta tsakiya, "dole ne mu ci gaba da bin ka'idojinmu, da kiyaye kasashenmu, da muradun al'ummarmu.

" Wannan Ziyara ta Assad a Hadaddiyar Daular Larabawa ta gudana ne watanni kadan bayan da Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa Abdullah bin Zayed Al Nahyan ya yi tattaki zuwa Damascus babban birnin kasar Syria, sannan kuma ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin yiwuwar komawar Syria cikin kungiyar kasashen Larabawa.

Tun bayan wannan ziyara ta shugaba Assad da ta gudana a jiya a kasar UAE, masana harkokion siyasar kasa da kasa suke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan yadda suke kallon lamarin ta mahanga daban-daban, musaman ma ganin cewa wannan ziyara ta Assad ta zo ne bisa gayyatar mahukuntan kasar ta UAE. Babban abin lura a nan shi ne, mahukuntan UAE sun gayyaci Assad zuwa kasarsu ‘yan kwanaki bayan ziyarar da sarkin Qatar Tamim Ben Hamad Al-khalifa Al-Thani ya kai kasar Amurka ne, inda ya gana da shugaban Amurka Joe Biden a fadar White House, wanda masana harkokin siyasar kasa da kasa ke kallon hakan a matsayin wani sako na musamman ga manyan kawayen Amurka a yankin wato Saudiyya da kuma UAE.

Daya daga cikin abubuwan da Biden ya bayyana a lokacin ziyarar sarkin Qatar na cewa, kasar Qatar ita ce babbar aminiyar Amurka a harkokin tattalin arziki a yankin, hakan ya bakanta wa Saudiyya da UAE, musamman ma kasantuwar cewa Qatar kasa ce da suke takun saka da ita, duk kuwa da cewa an yi sulhu na jeka-na-yi-ka a tsakaninsu. Duk da cewa kafin wannan lokacin bayan barkewar rikicin kasar Ukraine, da kuma matakin da Amurka ta dauka na saka takunkumi kan harkokin mai na kasar Rasha, ya yi tasiri wajen daga farashin danyen mai a kasuwanninsa na duniya, wanda kuma shakka babu hakan zai cutar da Amurka da kamfanoninta, wanda kuma kan hakan ne shugaban Amurka Biden ya tuntubi yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Ben Salman, da kuma yariman UAE mai jiran gado Muhammad Ben Zayed, domin sanar da su cewa su kara yawan danyen mai da suke hakowa, amma suka ki daukar wayarsa, kamar yadda jaridar wall Street Journal ta Amurka ta ruwaito.

A mahangar wannan jarida, wadannan jami’ai na Saudiyya da UAE sun ki daukar wayar Biden saboda matakin Amurka na kin nuna cikakken goyon baya kan yakin da suka suke kaddamarwa kan al’ummar Yemen, da kuma yin kira da a kawo karshen yakin, da kuma yadda gwamnatin Biden ta karkata ga batun cimma yarjejeniya da Iran a tattaunawar Vienna,a mahangar wannan jarida.

To sai dai wasu masanan suna ganin cewa, abin da yake aruwa baya rasa nasaba ne da alakar da ke tsakanin wadannan kasase da Amurka, da kuma tasirin siyasar jam’iyyu biyu na Amurka, wato Republican da kuma Democrat, inda kasashen Saudiyya da UAE sun fi dasawa da jam’iyyar Republican, wadda take goyon bayansu ido rufe tare da tashar makuden kudade daga hannunsu, yayin da kuma jam’iyyar Democrat sukan samu sabani da ita a kan batutuwa da dama a duk lokacin da take mulki.

Martanin ma’aikatar harkokin wajen Amurka kan ziyarar Bashar Assad a kasar hadaddiyar daular larabawa, yana a matsayin wata manuniya kan irin sabanin da ke akwai a tsakanin Amurka da UAE, kamar yadda kuma a lokacin da Amurka take kiran kasashen duniya da su kaurace wa Rasha, UAE ta tura ministan harkokin wajenta zuwa Moscow, inda ya gana da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov, tare da bayyana wa duniya matsayar UAE kan rikcin Ukraine, inda ministan harkokin wajen kasar ta UAE ya ce; Rasha tana da hakkin daukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaronta, wanda kuma wannan maganar ta bakantawa mahukuntan Washington matuka.

Koma dai yaya lamarin yake, abin da yake faruwa wata manuniya ce kan gagarumin canji da ake samu a cikin harkokin siyasar yankin gabas ta tsakiya, a kuma kasa da kasa, wanda hakan ba maslaha ce ga siyasar Amurka ta yankin da ma duniya ba, kuma masana suna ganin cewa, hakan yana kara nuna irin raunin da siyasar Amurka take yi ne a duniya, wanda zai cutar da tattalin arzikinta kai tsaye, da kuma rage karfin fada a ji da take da shi a duniya.

342/